Lamarin ya afku a Unguwar Sakkai karamar hukumar Faskari
A labarin da Katsina Daily Post News ke samu , na nuni da cewa wasu yan bindiga sun shiga kauyen Unguwar Sakkai dake cikin karamar hukumar Faskari, inda suka yi awon gaba da daliban wata makarantar islamiya a yayin da ake cikin dauka karatu.
Kamar yadda majiyarmu ta Katsina Post ta rawaito, lamarin ya afku ne a ranar Talata da yamma, daidai lokacin da daliban makarantar ke daukar darasi, inda suka kwashi dalibai 8 ciki har da malaminsu.
Sai dai da majiyar ta tuntubi Kakakin rundunar yan sandan jihar Katsina SP Gambo Isa, har kawo yanzun ba su kai ga samun ta bakinsa ba.