Tsohon Actony Ganaral Barr. Bala Silas Sanga yashiga sahu tareda daukar form na yin takaran Sanata a kudancin jahar AdamawaHon. Barr Bala Silas Sanga dai tsohon Kwamishina ne a ma'aikatar harkokin shara'a na jahar Adamawa, Bala dai ya sayi Form na neman takaran kujerar Sanata da zai wakilci kudancin jahar Adamawa.

Barr Bala dai masani ne kan harkokin Shari'a kuma ya bada gudummawar shi da dama akan harkokin Shari'a koda a shekara ta 2019 shine Kwamishina a ma'aikatar Shari'a na jahar Adamawa.

Kuma Barr Bala ya jagoranci manya manyan shara'a a jahar Adamawa dama Nigeria baki ɗaya wannan ya baiwa Barr damar samun ƙorewa tare da tuna hanyoyin taimakawa al'umma.

Bala dai zai shigo harkar siyasa ne kasan cewar irin gudummawar da yayi ta badawa a baya ko da ganin irin wasu damammaki da Bala ya samu a wasu lokuta da suka gabata, ya gina kotu a ƙananan hukumomi 2 dan sauwaƙawa mazauna wannan yankin zuwa wuraren shara'a.

Hasilama dai yana ƙoƙarin gabatar da wasu ayyuka da dama yanzu haka da zasu taimaki rayuwar jama'a Bala nada kyakkyawar alaƙa da wasu ƙungiyoyin ƙasashen waje da zasu iya taimakawa al'ummar.

Bala dai zai yi takara a ƙarƙashin inuwar jam'iyar APC Mai mulki a Najeriya ya kuma kammala dukkan nin shirye-shiryen tsayawa takaran, ya kuma samu goyon bayan jama'a matuƙa fata dai Allah yabada Sa'a da Nasara.

Post a Comment

Previous Post Next Post